Isa ga babban shafi
Syria-Amurka-Italiya

Amurka ta makaro bayan Tallafawa ‘Yan tawayen Syria-Masana

Kasar Amurka ta amince da kudirin tallafawa ‘Yan tawayen Syria da abinci da wasu kayan agaji amma masana suna ganin Amukar ta makaro domin har yanzu an kasa fito da hanyoyin magance rikicin kasar da ya lakume rayukan mutane sama 70,000.

Sakataren harakokin wajen Amurka, John Kerry yana ganawa da Shugaban 'Yan tawayen Syria Moaz al-Khatib kafin fara taron kawayen Syria a birnin Rome
Sakataren harakokin wajen Amurka, John Kerry yana ganawa da Shugaban 'Yan tawayen Syria Moaz al-Khatib kafin fara taron kawayen Syria a birnin Rome Reuters
Talla

Masu sa ido a rikicin Syria sun ce akalla mutane 100,000 ne suka mutu inda masana suke ganin a bi hanyar ruwan sanyi domin shugaba Assad ya amince ya mika mulki don kawo karshen zubar da jini a kasar.

A lokacin da ya ke ganawa da shugaban ‘Yan Tawayen Syria, Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry yace akwai sauran kudade Dala miliyan sittin da gwamnatin Obama ta yi alkawalin ba ‘Yan tawayen Syria.

Tun da farko, akwai tallafin kudi Dala miliyan 385 da gwamnatin Amurka ta ba kungiyoyin agaji su raba wa mutanen Syria.

Amma wannan ya sabawa wasu daga cikin ‘Yan tawaye wadanda suka yi zaton Amurka za ta taimaka ne da kayan yaki kamar yadda ta taimakawa ‘Yan tawayen Libya a 2011.

Dakta Aminu Umar na Babban kwalejin Fasaha ta Kaduna yace Syria ta fada yakin basasa gadan gadan, sai dai a jira a ga bangaren da zai samu nasara.

Salman Shaikh, Malamin Qatar yace yana da wahala Gwamnatin Assad ta sadaukar da mulkinta domin sai ta ga abinda ya “turewa Buzu nadi”

Wasu masana suna ganin Amurka tana fatar ‘Yan tawayen Syria za su samu nasara domin warware dangantakar kasar da Iran.

An dade ana zargin gwamnatin Iran tana taimakawa Gwamnatin Assad da makamai tare da tallafawa kungiyar Hezbollah domin kai doki ga Shugaban Syria Bashar Al Assad.

Yanzu haka shugabannin kasashe da suka kira kansu kawayen Syria suna gudanar da taro a Birnin Rome tare da ‘Yan tawaye da kuma wakilan gwamnatin Assad domin tattauna hanyoyin warware rikicin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.