Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Mutane 150,000 sun fice daga Syria-inji MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na cewa mutane akalla 150,000 ne suka fice daga kasar Syria cikin wannan watan, saboda kazancewar yaki tsakanin Dakarun Gwamnati da ‘Yan tawaye.

'Yan gudun Hijira da ke tserewa daga syria zuwa kasar Jordan
'Yan gudun Hijira da ke tserewa daga syria zuwa kasar Jordan REUTERS/Ali Jarekji
Talla

Wani karamin Sakatere na Majalisa Dinkin Duniya Jeffery Feltman ya fadawa kwamitin sulhu na majalisar cewa cin zarafin jama’a da Gwamnatin Shugaba Bashar Al-Assad na Syria babu dadin ji, domin yafi yadda bangaren ‘yan tawaye ke yi.

Mista Jeffery Yace duk da haka dukkan bangarorin da ke gwabza fadan na iya gurfana gaban kotun kasa-da-kasa da ke hukunta masu aikata manyan laifukan yaki.

Yace mutanen kasar akalla miliyan hudu yanzu haka suke bukatar agaji na gaggawa, domin daga ciki akwai mutane miliyan Biyu da suka rasa matsuguni a cikin kasar.

Bisa kididdigan Majalisar Dinkin Duniya an yi hasarar rayukan jama’a 70,000 da fara wannan fada kusan shekaru biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.