Isa ga babban shafi
Syria-Italiya

Taron sasanta rikicin Syria a birnin Rome

Shugabannin kasashen Duniya sun hallara a birnin Rome kasar Italiya domin tattaunawa da bangarorin da ke yaki da juna a Syria don fito da hanyoyin sasanta su bayan kwashe sama da shekaru biyu ana zubar da jini a cikin kasar.

Ministan harakokin Wajen Italiya Giulio Maria Terzi tare da Ministocin harakokin wajen kasashen Waje a birnin Rome
Ministan harakokin Wajen Italiya Giulio Maria Terzi tare da Ministocin harakokin wajen kasashen Waje a birnin Rome REUTERS/Remo Casilli
Talla

Kafin gudanar da taron, sabon sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya gana da shugaban ‘Yan tawayen Syria Ahmed Moaz al-Khatib.

Tun da Farko, kasar Amurka tace za ta taimakawa ‘Yan tawayen Syria da makamai don cim ma bukatar kawo karshen mulkin gwamnatin Bashar al Assad.

John kerry yace ‘Yan tawaye suna bukatar tallafi da taimako a yakin da suke gwabzawa da shugaba Bashar Assad.

Taron Birnin Rome na zuwa ne kwanaki biyu kafin ‘Yan tawayen Syria su gudanar da taron kafa gwamnati a Istanbul a ranar Assabar inda za su zabi Fira Minista da zai jagoranci yankunan da ‘Yan tawayen suka kwace daga ikon Gwamnatin Assad.

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande, ya bayyana fatar ganin an magance rikicin kasar Syria ta hanyar siyasa cikin makwanni masu zuwa.

A wata hira da ya yi da gidan radion Echo, da ke birnin Moscow, shugaban Francois Hollande yace, za su yi iya bakin kokarinsu a cikin makwanni masu zuwa don samo hanyar sisaya da za’a bi domin magance matsalar rikicin Syria da ke ci gaba da lakume rayukan al’umma.

Shugaban ya ce, takwaransa na Russia, Vladimir Putin yana da gagarumar rawar da zai taka wajen shawo kan shugaban kasar Syria, yayin da su ma za su bada tasu gudumawa wajen shirya tattauna wa tsakanin ‘Yan Tawayen Syria da gwamnati.

Kasar Faransa na bukatar shugagba Bashar al Assad ya sauka daga karagar mulki, yayin da Rasha ke adawa da shirin.

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane sama da mutane 7,000 tun kaddamar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Bashar Assad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.