Isa ga babban shafi
HIV

Cutar HIV na iya haifar da ciwon zuciya-Bincike

Wani bincike ya gano masu dauke da kwayar cutar HIV, na iya kamuwa da ciwon zuciya, da kashi 50 cikin 100 a wani gwajin da aka yi ga mutane fiye da dubu tabanin da biyu.

Kwayar Cutar Kanjamau da ke karya garkuwar jiki
Kwayar Cutar Kanjamau da ke karya garkuwar jiki DR
Talla

Binciken da likitoci suka gudanar ga akasarin maza, ya gano ciwon zuciya ya fi aukuwa ga mutanen da ke dauke da kwayar cutar HIV.

Binciken ya gano bayan canjin da ake samu sakamakon cutuka irinsu shan taba sigari da shan barasa da sauran abubuwan da ke janyo kasada, da suka hada da hawan jini da yawan kitse a jiki, mutanen da ke dauke da kwayar cutar ta HIV suna da kasadar kamuwa da ciwon zuciya, fiye da wadanda basu da shi da kashi 50 cikin 100.

Bincike daban daban da aka gudanar a baya, sun nuna sauyin da jikin dan adam ke samu, sakamakon kamuwa da kwayoyin cutar ta HIV, suna sa saurin tsufa kafin fara shan magani, lamarin da ke sa jikin ya kamu da cutukan da ke da alaka da tsufa.

Ko a watan Yulin bara, wani binciken ya gano cewa, kasadar masu dauke da kwayoyin cutar HIV ta kamuwa da ciwon zuciya, ta ninka wadanda ba su dauke da ita, sakamakon kunburar da hanyoyin jinin su ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.