Isa ga babban shafi
Faransa

Likitocin Faransa suna nazarin samar da wata allurar rigakafin cutar AIDS

Likitocin Faransa na shirin gwajin wata sabuwar allurar rigakafin cutar AIDS KO SIDA, da aka gano a kasar, ana kyautata zaton za ta yi tasiri, a kokarin da ake yi, na rage illolin cutar a duniya.

Farfes Erwann Loret wanda ke gudanar da binciken samar da sabuwar aluurar rigakafin cutar Sida ko Aids a Faransa
Farfes Erwann Loret wanda ke gudanar da binciken samar da sabuwar aluurar rigakafin cutar Sida ko Aids a Faransa REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Nan da ‘Yan makwanni masu zuwa ne za a soma gwajin allurar a kan wasu mutane 48 da ke dauke da kwayoyin cutar a garin Marseille na kudancin kasar Faransa.

Farfesa Erwann Loret, daya daga cikin likitocin da suka gano wannan sabuwar allurar rigakafi, ya ce duk da ya ke rigakahin ba wai zai kawo karshen HIV ko kuma SIDA ba ne a duniya, amma zai rage kaifi da kuma illar cutar a jikin wanda ke dauke da kwayoyinta, kuma tuni hukumar tabbatar da ingancin magunguna ta Faransa ta amince da soma yin gwajin.

Bayan soma amfani da shi kamar yadda wadanda suka hada shi ke cewa, sai bayan watanni Biyar ne za a iya tabbatar da inganci ko kuma rashin ingancinsa a kan masu dauke da kwayoyin cutar, to sai dai allurar za a yi wa ma su dauke da kwayar cutar ita ne sau uku jere a juna, Allura daya a kowane wata.

A shekara ta 2011, kimanin mutane milyan 34 ne ke fama da wannan cutar a duniya, kuma daga lokacin soma bayyanarta zuwa yau, HIV ta kashe mutane akalla milyan 30 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.