Colombia
Gwamnatin Colombia za ta fara zaman tattaunawa da ‘Yan tawayen
Tawagar Gwamnatin kasar Colombia, a wajen taron sasantawa da ‘Yan Tawayen kungiyar FARC, ta isa Havana, Cuba, don fara tattaunawa yau. Shugaban tawagar, Humberto de la Calle, yace lokaci ya yi da ‘Yan Tawayen za su nuna cewar da gaske suke, don cim ma yarjejeniyar kawo karshen yakin da ake da su.
Wallafawa ranar:
Talla
An kwashe tsawon shekaru da dama ana rikici a kasar Colombia, wanda ya yi sanadiyar dubban mutune tare da raba miliyoyin mutane da gidajensu.
Dukkaninin Bangarorin biyu sun bayyana fatar samun nasara a tattaunawar da za su fara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu