Isa ga babban shafi
Tunisia-libya

Tunisia: Mutane 54 sun halaka a hadarin jirgin ruwa

Matsanancin kishin ruwa da yunwa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 54 da ke cikin wani jirgin ruwa a tsakiyar tekun kasar ta sagake.

Wani jirgin ruwa  a kan teku
Wani jirgin ruwa a kan teku
Talla

Mutun daya da rayu daga cikin wannan jirgin ruwa, Abbes Settou, masu aikin ceto su ka tsamoshi bayan ya yi ta kwankwadan ruwan tekun.

Dukkanin su dai bayanai na nuna bakin haure ne da suka taso daga tashan jirgin ruwa dake Tripoli na kasar Libya.

Haka kuma a cikin wadanda su ka mutu har da mata guda goma.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya rawaito cewa mutanen sun kasa neman taimakon gaggawa domin na’urar aika sakon jirgin ta lalace.

A cewar Settou, sun riga sun kai yankin kasar Italiya a kan ruwan amma basu samu taimako ba domin na’urar sadarwar ta lalace.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi kiyasin cewa akalla mutane 170 aka nema aka rasa a yayin da suke kokarin tsallakawa daga kasar Libya zuwa nahiyar Turai a wannan shekarar.

Kasashen Italiya da Girka sune hanyoyi mafi sauki da bakin haure kan yi amfani da su wajen shiga kasashen Turai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.