Isa ga babban shafi
Brazil-Amurka

Brazil da Amurka zasu inganta huldar kasuwanci

Shugaban kasar Vrazil Dilma rousseff zata kai ziyarar farko zuwa kasar Amurka domin tattauna bututuwan da suka shafi inganta huldar kasuwanci da ilimi da huldar Diflomasiya.

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff
Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Kasar Brazil ita ce kasa ta shida a habakar tattalin arzikin duniya, kuma kasa ta Takwas da ke huldar kasuwanci da kasar Amurka.

Amma kasar Brazil tana neman goyon bayan Amurka ne a kudirinta na neman kujerar din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

A yau Litinin ne ake sa ran shugaba Rousseff zata gana da Shugaban kasar Amurka Barack Obama a fadar White house.

Ana sa ran  ganawar shugabannin biyu zasu mayar da hankali wajen inganta huldar kasuwancinsu da ci gaban ilimi tsakanin kasashen biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.