Isa ga babban shafi
IMF

Hukumar Lamuni zata samar da kudade domin ceto Turai

Hukumar bada lamuni ta duniya IMF, tace zata samar da kudaden da suka kai Dalar amurka Biliyan 500, domin ceto tattalin arzikin kasashe, a daidai lokacin da matsalar tattalin arzikin turai ke barazana ga kasashen duniya.

Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya Christine Lagarde, a lokacin ziyararta Najeriya
Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya Christine Lagarde, a lokacin ziyararta Najeriya © Reuters/Stephen Jaffe
Talla

Sanarwar ta zo ne bayan da ‘yan kwamitin gudanrawar hukumar suka yi wani taron da suka tattauna kan karfin da asusun bada lamunin ke da shi domin bayar da tallafi ga kasashen duniya.

Asusun yace kididdigar da ma’aikkatan shi suka yi ta nuna cewa akwai bukatar kudaden da suka kai dala Tiriliyan daya a shekara mai zuwa, don haka ne zai samar da dala Biliyan 500, bayan samar da hanyoyin bayar da bashi.

Yayin da kasashen Turai da dama ke afkawa cikin matsalar tattalin arziki, a daidai lokacin da kasar Girka ke gab da kasa biyan nata bashin, hukumar IMF tace babu isassun kudaden da zata iya ceto tattalin arzikin kasashen duniya.

Shugabar hukumar IMF Christine Lagarde, tace kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20 ta nemi a gudanar da taro, kuma hukumar ta duba muhimmancin warware matsalar tattalin arzikin duniya, tare da kawo karshen kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta.

A baya, hukumar ta bayyana cewa zata rage darajar hasashen da ta yi game da tattalin arzikin kassashen duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.