Iraqi-Amurka
Gwamnatin Iraqi ta kama hanyar rugujewa inji Biden
Mataimakin Shugaban kasar Amuka, Joe Biden, yace Gwamnatin kasar Iraqi, ta kama hanyar rugejewa, sakamakon barakarar da aka samu tsakanin Fira Minista Nuri al Maliki mabiyin Shia, da Mataimakin shugaban kasa, Tariq al Hashemi, mabiyin Sunni.
Wallafawa ranar:
Talla
Biden yace rashin taka tsan-tsan tsakanin bangarorin biyu, na iya haifar da tashin hankali a kasar, kamar yadda aka samu a shekarar 2006-2007 inda aka kashe dubban mutane.
Yanzu haka Hashemi ya samu mafaka a Yankin Kurdistan mai cin gashin kansa, bayan umurnin kama shi da Fira Ministan ya bayar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu