Isa ga babban shafi
Amurka-Myanmar

Suu Kyi ta gana da Clinton tare da fatar inganta Demokradiyya a Myanmar

Shugabar adawar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta bayyana fatar samun sauyin demokradiya a kasar, bayan ganawa da Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton.

Hillary Clinton tare da Shugabar Adawar kasar Myanmar
Hillary Clinton tare da Shugabar Adawar kasar Myanmar REUTERS/Saul Loeb
Talla

Suu Kyi da ke shirin takarar kujerar Majalisa, tace muddin suka hada kai, suna iya cim ma burin su a kasar.

Shugabar adawar ta gana ne da Clinton lokacin Karin safe, inda Clinton it ace babbar Jami’a daga Amurka da ta kai ziyara Myanmar tun bayan shekaru 50 da suka gabata.

Bayan ganawarsu, Aung San Suu Kyi tace zasu yi aiki tare domin ci gaba da inganta demokradiyya a cikin kasar.

Sai dai kasar amurka tace zata ci gaba da tsaurara takunkumi ga tsoffin shugabannin kasar da suka kwashe shekaru suna mulki kafin mika mulki ga gwamnatin farar hula a bara.

Clinton tace shugaba Obama ya gamsu da sauye sauyen da Gwamnatin Myanmar ke yi a siyasar kasar, kuma suna fatar ganin matakin ya dore.

A jiya laraba ne , Hillary Clinton, ta fara ziyarar aiki a kasar Myanmar, ziyara irin ta ta farko daga wani babban jami’in kasar Amurka, a cikin shekaru sama da 50 da suka gabata.

Clinton ta gana da takwaranta, Wunna Maung Lwin, a Napydow, inda daga bisani ne kuma ta gana da shugaban kasa Thein Sein.

A baya-bayan nan ne Aung San Suu Kyi ta yi rijistar Jam’iyyarta ta NLD domin tsayawa takarar ‘Yar Majalisa a zaben da za’a gudanar a cikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.