Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa-Amurka

Koriya ta Arewa ta sake wani gwajin makami

Kasar Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai cin dogon zango ba tareda ta samu nasara ba a cewa rundunar tsaron kasar Amurka.

Wasu daga cikin makaman masu cin dogon zango
Wasu daga cikin makaman masu cin dogon zango AFP PHOTO / POOL / ROLEX DELA PENA
Talla

Duk da yake akwai dokoki dake haramta gwaji dama harba makami mai cin dogon zango,Koriya ta arewa na ci gaba da gwaje gwajen ta ,an dai bayyana cewa makamin da ta harba a baya baya nan zai iya cimma sansanin dakarun Amurka dake arewacin Pacifik.

Mai Magana da yahu ma’aikatar tsaron Amurka Gay Ross ya na mai cewa wanan sabon harbi na a matsayin tsokana daga Koriya ta Arewa, ya kuma yi gargadi zuwa hukumomin Pyongyang da su dakatar da duk wani gwaji wanda hakan zai taimakawa wajen samu zaman lafiya a yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.