Isa ga babban shafi
Syria-Geneva

An kasa jituwa tsakanin Gwamnati da ‘yan tawayen Siriya a Geneva

A taron sasanta rikicin kasar Syria da ake gudanarwa a birnin Geneva, babu wani ci gaba da aka samu a zaman sulhu da ake yi tsakanin wakilan Gwamnatin shugaba Bashar al-Assad da na ‘Yan adawa masu samun goyon bayan kasashen Yammaci domin kawar da Gwamnati

Taron Geneva
Taron Geneva REUTERS/Fabrice Coffrini/
Talla

Babban mai shiga tsakanin bangarorin biyu na Majalisar dunkin Duniya a rikicin Syria Lakhdar Brahimi yace babu wani ci gaba da aka samu amma za su ci gaba da tattaunawa akan batun sauyin gwamnatin shugaba Assad na Syria.

‘Yan adawar na Syria sun ce kananan Jami’an gwamnati ne Assad ya tura zaman tattaunawar. Kamar yadda Louay Safi daya daga cikin shugabannin ‘Yan adawar ke cewa .

A bangaren wakilan gwamnati kuma Buthaina Shaaban tace gina sabuwar kasar Syria shi ne babban muradin su.

Yace magance matsalar shi ne muradinmu tare da dawo da ‘Yan gudun hijira da gina Syria, wannan shi ne banbancin mu da wadanda ke son a shigo ayi abin da ake son yi a Syria.

A taron dai wakilan Gwamnatin shugaba Bashar al-Assad sun gabatar da wasu bukatu da bangaren 'yan tawayen kasar suka ki amincewa abinda ya tada hayaniya, kuma mai shiga tsakani na Majalisar dunkin Duniya Lakdra Brahimi, ya dakatar da tattaunawar kai tsaye.

'Yan tawayen dai na ganin cewar duk wata magana da ba ta canja Gwamnatin bashar al-Assad ba, to a wurinsu ba karbabbiya ba ce.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.