Isa ga babban shafi
UNESCO-Falesdinu-Amurka

Amurka ta janye Tallafinta a UNESCO bayan amincewa da Falesdinu

Gwamnatin Amurka ta janye tallafin da take bayarwa ga UNESCO hukumar Majalisar Dunkin Duniya ta al’adu bayan hukumar ta yi watsi da bukatar kasar da Isra’ila na kin amincewa da bukatar Falesdinawa.Tallafin Amurka a UNESCO kusan shi ne rabin kasafin kudin hukumar a shekara, kuma Amurka ta yi gargadi ga sauran hukumomin Majalisar Dunkin Duniya kan daukar irin wannan matakin idan har suka bi sahun UNESCO.A cewar Victoria Nuland kakakin gwamnatin Amurka, a watan Nuwamba ne ya dace ace kasar ta bada tallafin kudi dala Miliyan $60 ga UNESCO amma yanzu Amurka zata haramtawa hukumar Tallafin.Tuni dai Falasdinu ta samu wakilci a UNESCO, sakamakon kuri’u 107 da ta samu, daga 173, yayin da 14 a karkashin jagoranci Amurka da Isra’ila suka ki amincewa, 52 kuma suka kauracewa zaman taron hukumar.Kasar Faransa ce ta jagoranci kuri’ar amincewa tare da kasashen larabawa da kasashen China da Indiya da kuma kasashen yankin Latin Amurka.Kasar Isra’ila da Amurka da kasar Canada da Australiya da kasar Jamus ne suka kada kuri’ar kin amincewa, kasar Japan kuma da Birtaniya suka kauracewa zaman taron hukumar.Yanzu haka Fira Ministan Isra’ila Benjamin Natenyahu ya kira wani taron gaggawa tsakanin shi da ministocinsa domin tattauna yadda zasu yi kokarin mayar da martani kan Nasarar da Falesdinu ta samu a UNESCO. 

Shugaban Amurka Barak Obama
Shugaban Amurka Barak Obama AFP
Talla

03:29

Farfesa Mainoma

Dangane da bijerewar da kasashen duniya suka yi akan bukatar Isra’ila da Amurka, Farfesa Muhammad Mainoma na Jami’ar Nasarawa a Najeriya yace matsalar tattalin arzikin da ya shafi Amurka shi ya sanya kasar ke kokarin katse kudaden da take bayarwa a Majalisar Dunkin Duniya domin sasanta rikicin da ke addabarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.