Isa ga babban shafi
UNESCO-Palestine

An kada kuri’ar amincewa da Palesdinawa a UNESCO

A yau litinin ne hukumar Ilimi, Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta kada kuri’ar amincewa da Palesdinu.Daga cikin Kasashe 173, 107 sun amince, 14 sun hau kujerar MUN KI, yayin da fiye da 40 suka yi rowar kuri'un su.tuni kasar Amurka ta yi barzanar katse tallafin da take baiwa hukumar ta UNESCO, in har ta amince da Palasdinawan.Kada kuri’ar a UNESCO ya zo ne dai dai da lokacin da Riyad al-Malki ministan harakokin wajen Palesdinu zai gabatar da jawabi a zauren taron hukumar.Tuni dai Darekta Janar na hukumar Irina Bokova ta bayyana fargabarta na yiyuwar janyewar tallafin kasar Amurka idan har aka amince da bukatar Palesdinawa.A cewar ta idan har hakan ya tabbata dole hukumar ta dakatar da wasu shirye shiryenta tare da datse kasafin kudin hukumar na shekara.Tun a ranar Talata ne hukumar  ta UNESCO ke gudanar da taro a birnin Paris na kasar FaransaA shekarar 2003 ne kasar Amurka ta sake dawowa a UNESCO bayan kauracewa hukumar a shekarar 1984 bayan mahukuntar kasar sun ga muradun hukumar na karo da juna da huldar diflomasiyar Amurka.Sai dai Shugaba Barrack Obama yana ganin hukumar UNESCO wata hanya ce ta cim ma muradun kasashen waje tare da yada al’adunsu.Yanzu haka jekadan kasar Isra’ila Nimrod Barkan ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa zasu bi sahun Amurka domin janye tallafin kudaden da suke bayarwa ga hukumar UNESCO.

Taron hukumar UNESCO ta Majalisar Dunkin Duniya a birnin Paris.
Taron hukumar UNESCO ta Majalisar Dunkin Duniya a birnin Paris. Reuters/Benoit Tessier
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.