Isa ga babban shafi

WHO ta amince da sabuwar allurar rigakafin Kwalara

Hukumar lafiya ta duniya ta amince da yin amfani da wani sabon nau’in allurar rigakafin cutar amai da gudawa daidai lokacin nan da duniya ke fama da karancin alurarar rigakafin cutar.

Wani ƙaramin yaro da ke ƙarban allurar rigakafin cutar amai da gudawa
Wani ƙaramin yaro da ke ƙarban allurar rigakafin cutar amai da gudawa AP - Hani Mohammed
Talla

Ana sa ran sabuwar allurar mai suna Euvichol-S, ta taimaka wajen rage yawan masu kamuwa da cutuka dake da alaka da gurbatatten abinci da ruwan sha da kuma muhalli.

WHO da ta amince da sahihancin sabuwar allurar riga-kafin Euvichol-S, ta ce cikin sauki aka samar da ita, kuma ba ta da tsada, haka ma za a iya samar da adadi mai yawa cikin ƙankanin lokaci.

Hukumar ta yi kira ga kungiyoyi masu ba da agaji a kan abinda ya shafi riga kafi kamar Gavi da kuma asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF cewa su rika siya wa ƙasashe matalauta.

Karancin allurar rigakafin cutar kwalara ya jefa ƙasashe da dama musamman a nahiyar Afrika cikin wani yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.