Isa ga babban shafi

Kotu ta sake dage zaman shari'ar Jacob Zuma a kokarinsa na tsayawa takara

Kotu a birnin Johannesburg na Afrika ta kudu ta dage zaman sauraron shari’ar da ta faro kan tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, shari’ar da tsohon jagoran ya nema da kansa bayan tun farko ya samu nasara a shari’ar da ta wanke shi daga tuhume-tuhumen da suka haramta masa tsayawa takara.

Tsohon shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma bayan fitowa daga babbar kotun kasar da ke birnin Johannesburg a jiya Alhamis.
Tsohon shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma bayan fitowa daga babbar kotun kasar da ke birnin Johannesburg a jiya Alhamis. AFP - EMMANUEL CROSET
Talla

Zuma wanda ke son kalubalantar shugaba Cyril Ramaphosa a zaben kasar da ke tafe cikin watan gobe, tun da wur-wuri ya bayyana gaban kotun ta birnin Johannesburg, zaman da ya gudana karkashin jagorancin manyan alkalai gabanin dage shi zuwa 6 ga watan Agustan shekarar nan.

Bayan shari’ar farko da kotun ta kore duk wasu tuhume-tuhume da a baya suka haramtawa tsohon jagoran iya tsayawa takara, a yanzu Zuma na son kotun ta yi hukunci kan zargin da ya ke yiwa shugaba Ramaphosa da yi masa manakisa.

Zuma na son hukunta Ramaphosa ne kan abin da ya kira biris da yadda masu shigar da kara da kuma ‘yan jarida suka bankado bayanan lafiyarsa tare da fallasasu duk kuwa da yadda hakan ya sabawa dokokin shigar da kara.

Mai shari’a Norman Manoim da ya jagoranci zaman na jiya Alhamis ya ce sai zuwa ranar 6 ga watan Agusta ne kotun za ta ci gaba da shari’ar don biya Zuma hakkinsa kan tuhumar shugaban mai ci Cyril Ramaphosa.

Bayan fitowarsa daga zaman kotun, Jacob Zuma ya gabatar da jawabi gaban dandazon magoya bayansa tare da shan alwaashin kai labari a zaben kasar na ranar 29 ga watan Mayu karkashin sabuwar jam’iyyar da kafa ta uMkhonto we Sizwe da ake yiwa lakabi da MK.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.