Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Kotun Afrika ta Kudu ta umarci tsohon shugaban kasar Zuma ya koma kurkuku

Wata kotu a Afirka ta Kudu ta bayar da umarnin mayar da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma gidan yari, lamarin da ya kawo karshen izinin tafiya jinya da aka ba shi a watan Satumba.

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, 4/07/21.
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, 4/07/21. AFP - EMMANUEL CROSET
Talla

Cikin sa’o’I da wannan hukunci, lauyoyin Mista Zuma, suka gabatar da bukatar daukaka kara, wanda ke nufin tsohon shugaban ba zai koma gidan yari ba har sai an saurari karar da suka daukaka.

A cikin karar da suka shigar, lauyoyinsa sun ce hukuncin da kotun ta yanke zalunci ne da kuma wulakanta tsohon shugaban ba tare da la’akari da halin rashin lafiyar da yake ciki ba, kuma hakan bashi da maraba da take hakkin dan adam.

Zuma, mai shekaru 79, an daure shi ne a watan Yuli na tsawon watanni 15, bayan da ya ki bayar da shaida ga masu binciken cin hanci da rashawa.

Daurin da aka yi masa ya haifar da tarzoma da sace-sace a lardinsa na KwaZulu-Natal wanda ya bazu zuwa Johannesburg a watan Yuli, inda aka kashe sama da mutane 350.

Wannan dai shi ne tashin hankali mafi muni a Afirka ta Kudu tun bayan kawo karshen mulkin ‘yan tsirarun farar fata a shekara ta 1994.

Baya ga binciken da wani kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na musamman ke gudanarwa a kansa, Mista Zuma yana kuma fuskantar wata shari'ar cin hanci da rashawa da ta shafi sayan makamai daga wasu kamfanoni biyar na Turai a shekarar 1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.