Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Jami'an tsaron Afirka ta Kudu sun kame wasu magoya bayan Zuma dake zanga-zanga

Jami’an tsaron Afirka ta Kudu, sun cafke mutane 62 a zanga-zangar da ta barke a sassan kasar biyo bayan tsare tsohon shugaba Jacob Zuma.

Wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma dake zanga-zangar neman sakin sa 3 ga watan Yuli 2021.
Wasu daga cikin magoya bayan tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma dake zanga-zangar neman sakin sa 3 ga watan Yuli 2021. REUTERS - ROGAN WARD
Talla

Zanga-zangar wadda ta fara daga yankin Kwazulu-Natal da ke matsayin cibiyar magoya bayan Zuma, daga bisani ta yadu zuwa sassan kasaar ciki har da Johannesburg birni mafi girma a kasar ta Afirka ta Kudu.

Masu zanga-zangar sun kona tayoyi da kuma datse manyan tituna, yayin da wasu daga cikinsu suka rika fasa shaguna da kuma wawashe dukiyoyin jama’a, yayin da wasu ke rera taken nuna goyon baya ga tsohon shugaba Zuma.

To sai dai yayin da magoya bayan Jacob Zuma suka lashi takobin ci gaba da wannan tarzoma har sai zuwa lokacin da aka saki tsohon shugaban, wasu bayanai na cewa wasu daga cikin mazu zanga-zangar na bayyana bacin ransu ne dangane da halin talaucin da suke fama da shi.

A wannan Litinin dai ne Kotun Kolin kasar za ta yi zama na musamman don duba bukatar da Zuma ya gabatar, inda yake neman a sassauta hukuncin daurin watanni 15 da aka yanke masa saboda samun sa da laifin kin mutunta umurnin kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.