Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Magoya bayan Zuma na gudanar da boren neman sakin sa daga kurkuku

Magoya bayan tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma sun bukaci sakin shi daga gidan yarin da ya ke tsare bayan mika kanshi ga mahukuntan kasar a makon jiya, kiraye-kirayen da ke zuwa bayan tsanantar tashe tashen hankula a yankin KwaZulu-Natal.

Magoya bayan tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Magoya bayan tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma © (Photo by Emmanuel Croset / AFP)
Talla

Tun daga shekaran jiya juma’a ake fuskantar tashin hankali a yankin na KwaZulu-Natal da ke matsayin mahaifar Jacob Zuma, inda magoya bayan tsohon shugaban suka rika kone konen kayakin gwamnati da na daidaikun mutane don nuna fushinsu kan tsare Zuma.

A larabar da ta gabata ne, Jacob Zuma ya mika kanshi ga jami’an tsaro, mintuna kalilan gabanin cikar wa’adin da aka dibar masa na bayyana gaban mahukunta don fara wa’adin watanni 15 da Kotu ta yanke masa a gidan yari bayan samunsa da laifin kin mutunta kotu yayin shari’ar da ake masa game da almundahanar da ta dabaibaye mulkinsa tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018.

Wasu ganau sun bayyana cewa magoya bayan na Zuma na ci gaba da kone kone a sassan kasar tare da barazanar fadada tashe-tashen hankulan matukar ba a saki tsohon shugaban ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.