Isa ga babban shafi

Jacob Zuma ya kammala wa'adin watanni 15 a gidan yarin Afrika ta kudu

Tsohon shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma ya kammala wa’adin da kotu ta dibar masa na zaman yarin watanni 15 sakamakon raina umarnin kotu.

Jacob Zuma, tsohon shugaban Afrika ta kudu.
Jacob Zuma, tsohon shugaban Afrika ta kudu. AFP - EMMANUEL CROSET
Talla

Jacob Zuma ya fuskanci hukuncin ne bayan da ya ki bayyana gaban kotu duk da sammacin da aka aika masa lokacin da ake masa shari’a kan zargin rashawa.

A ranar 7 ga watan Yulin bara ne Zuma ya mika kansa ga jami’an tsaro bayan tsanantar rikici a kasar da ya kai ga asarar tarin rayuwa sakamakon yadda magoya bayansa suka ki amincewa da matakin kama shi.

Rikicin na lokacin kamen Zuma dai na matsayin tashin hankali mafi muni da Afrika ta kudu ta gani a baya bayan nan.

A jawabinsa bayan kammala cinye wa’adin na watanni 15, Zuma ya ce ya matukar jin dadi bayan zamowa mai cikakken ‘yanci, yayinda ya godewa magoya bayansa.

A cewarsa Zuma sakwannin magoya bayan da ya ke gani a shafukan sada zumunta ne suka kara masa kwarin gwiwa wajen ganin bai baiwa magoya bayansa damar yin nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.