Isa ga babban shafi

An kama mutane 13 biyo bayan kisan dan adawa a Habasha

'Yan sandan Habasha sun kama wasu mutane 13 da ake zargi da hannu a kisan da aka yi a daren ranar talata zuwa laraba wani dan adawar kasar mai fada a ji a yankin Oromia.

Bate Urgessa, dan siyasa bangaren adawa da aka kashe a Oromia
Bate Urgessa, dan siyasa bangaren adawa da aka kashe a Oromia © DR
Talla

Dan siyasar mai suna Bate Urgessa, mai shekaru 41, shugaban kungiyar 'yan adawa ta Oromo Liberation Front (OLF), jam'iyyar adawa mai rijista bisa doka, an same shi a ranar Laraba da safe, an harbe shi har lahira a Meki, wani gari mai tazarar kilomita 150 da ke kudancin birnin  Addis Ababa babban birnin kasar, yana mai magana da yawun jam'iyyarsa.

Tariku Dirbaba, babban jami'in 'yan sanda na  shiyyar Shoa ta gabas inda Meki yake "ya nuna cewa an kafa wani sashin bincike don gudanar da bincike kan kisan Bate Urgessa" kuma "an riga an kama mutane goma sha uku", kamar yadda kafar yada labarai ta Oromia ta ruwaito. Ba a bayar da cikakken bayani kan sunayen wadanda ake zargin ba.

Sojojin Habasha yayin kokarin tabbatar da doka da oda a garin Bisoftu na yankin Oromia, bayan kafa dokar ta baci a shekkarar 2016.
Sojojin Habasha yayin kokarin tabbatar da doka da oda a garin Bisoftu na yankin Oromia, bayan kafa dokar ta baci a shekkarar 2016. AP - STR

Yankin mafi girma kuma mafi yawan jama'a na kasar Habasha, Oromia yana cikin wani mummunan tashin hankali da aka murkushe shi tun shekara ta 2018, tare da kashe-kashen al'umma.

Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Habasha (EHRC), wata cibiya ce ta jama'a amma mai cin gashin kanta bisa ka'ida, ta yi kira da a yi "bincike cikin sauri, rashin son kai da cikakken bayani" kan wannan kisan "domin a hukunta wadanda ke da hannu"

Wasu daga cikin masu adawa da gwamnatin Habasha na yankin Oromia.
Wasu daga cikin masu adawa da gwamnatin Habasha na yankin Oromia. Reuters

Jakadan Tarayyar Turai (EU) a Habasha, Roland Kobia, da takwaransa na Birtaniya Darren Welch da ofishin Ma'aikatar Harkokin wajen Amurka ta Afirka sun yi tsokaci kan kiran da Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Habasha ta yi na gudanar da bincike kan kisan  Bate.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.