Isa ga babban shafi

Majalisar dokokin Habasha ta amince da nadin sabon mataimakin Firaministan kasar

‘Yan majalisar dokokin kasar Habasha sun amince da nadin shugaban hukumar leken asiri Temesgen Tiruneh a matsayin mataimakin firaminista Abiy Ahmed, a wani gagarumin sauyi da aka samu a daidai lokacin da kasar ke fama da rikice rikicen cikin gida.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan. AP - Mulugeta Ayene
Talla

A wani bangare kuma, an nada mai taimakawa Abiy kan manufofin kasashen ketare Taye Atske Selassie a matsayin ministan harkokin wajen kasar, yayin da mai ba da shawara kan harkokin tsaro Redwan Hussein ya maye gurbin Temesgen a matsayin shugaban hukumar leken asiri da tsaro ta NISS.

A yayin da ofishin Abiy ya bayyana manyan sauye-sauyen a matsayin wani mataki na inganta yanayin jagorantar al'umma, a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Twitter.

Ana dai kallon Temesgen a matsayin nagartacce, kuma na hannun daman firaminista Abiy, wanda ya zabe shi a wasu muhimman mukamai a lokutan da kasar ke fama da rikici.

Kasa ta biyu mafi yawan al'umma a Afirka, mai mutane kusan miliyan 120, a halin yanzu tana fama da kalubale da dama, da suka hada da tashe-tashen hankula a yankuna da dama, da karancin abinci da kuma matsalolin tattalin arziki.

Har ila yau Habasha ta fuskanci tashin hakali a yankin bayan cimma yarjejeniya a watan Janairu bayan da ta kulla yarjejeniya da yankin Somaliland dake fafutukar ballewa daga jikin Somaliya a kokarin ta na samun mikakkiyar hanya ta amfana da tekun bahar Maliya kai tsaye.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.