Isa ga babban shafi

An yi wa wani fitaccen dan siyasar Habasha kisan gilla a Oromia

An gano gawar wani fitaccen dan siyasar Habasha da aka harbe a yankin Oromia, sa’o’i kalilan bayan kama shi da sojojin kasar suka yi.

Taswirar kasar Habasha
Taswirar kasar Habasha © Ethiopia Simon MALFATTO AFP
Talla

A watan Maris din da ya gabata kotu ta bayar da belin Bate Urgessa wanda jigo ne a jam’iyyarsa ta Oromo Liberation Front (OLF), bayan tsare da shi tsawon wasu kwanaki da aka yi tare  da wani dan jaridar Faransa Antoine Galindo.

Jami’an tsaro sun sake cafke fitacccen dan siyasar mai shekaru 41 ne kuma a ranar Talatar da ta gabata, inda suka yi awon gaba da shi daga wani Otal da ke garin Meki da ke kudu da birnin Addis Ababa.

Kakakin jam’iyyar OLF Lemi Gemechu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar da fari sun samu labarin cewa jami’an tsaron da suka kama Urgessa sun  tsare shi ne a wani gidan Yari da ke garin na Meki, sai dai daga bisani iyalansa suka tabbatar da labarin gano gawarsa da aka yasar da raunin harbin bindiga da safiyar Larabar nan.

Har zuwa lokacin wannan wallafa dai gwamnatin Habasha ba ta ce komai kan lamarin ba, yayin da iyallai da kuma jam’iyyar OLF suka kasa tantance cewar jami’an tsaron da suka kama Urgessa na gwamnatin Tarayyar kasar ne kuma na mahukuntan yankin na Oromia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.