Isa ga babban shafi

Habasha ta kama wani dan jaridar kasar Faransa da ya halarci taron AU

Hukumomi a Habasha sun kama wani dan jaridar mai suna Antoine Galindo Dan kasar Faransa bisa zargin sa da yunkurin kawo hargitsi vayan halarci taron shugabannin kasashen Afirka na AU.

Taswirar kasar Habasha.
Taswirar kasar Habasha. © RFI
Talla

Jaridar “The specialist publication Africa Intelligence” ta sanar da cewa, ta tura ma’aikacinta ne zuwa Habasha wadda Galindo ke yiwa aiki domin tattara bayanai kan taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a farkon wannan wata.

Bayan kama shi a ranar Alhamis, an kuma gurfanar da shi a gaban Kuliya, inda kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi har zuwa daya ga watan Maris da za a ci gaba sauraron shari’ar.

To sai dai Jaridar “The Specialist” ta ce ba bu wata hujja da za ta sa a ci gaba da tsare ma’aikacinta a gidan yarin har tsawon wannan lokaci, domin a cewarta hukumomi sun san da zuwan sa kuma  su ne suka ba shi izinin gudanar da aiki a cikin kasar.

Wani shaidar gani da ido da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, jami’an tsaro sun kama Galindo ne a wani Otel da ke Addis Ababa babban birnin kasar yayin ganawa da daya daga cikin jiga-jigan ‘yan jam’iyyar adawa ta OLF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.