Isa ga babban shafi

Mutane fiye da 90 sun mutu bayan nutsewar kwale-kwalensu a Mozambique

Mahukuntan Mozambique sun tabbatar da mutuwar mutane fiye da 90 bayan wani jirgin kwale-kwale mai dauke da mutane 130 ya nutse a jihar Nampula ta areacin kasar.

Hotunan Jiragen kwale-kwale a ruwan Mozambique.
Hotunan Jiragen kwale-kwale a ruwan Mozambique. Getty Images - Eddie Gerald
Talla

Babban sakataren jihar Nampula Jaime Neto da ke tabbatar da faruwar ibtila’in a jiya Lahadi, ya ce zuwa yanzu an tsamo gawarwakin mutane 91 kuma ana laluben wasu da suka bace.

Rahotanni sun ce jirgin wanda na masunta ne ya dauki fasinjan da suka wuce kima a kokarin tsallakar da su zuwa wani tsibiri da ke gefen birnin na Nampula amma kuma ya gamu da tangarda a hanya.

A cewa Jaime Neto kananan yara su ne galibin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin kwale-kwalen sakamakon yadda suka gaza ninkaya dalilin da ya kai ga nutsewarsu.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mutanen da ke cikin birnin na kokarin tserewa zuwa kananun tsibirai ne saboda bayanan karya da ke yaduwa kan annobar kwalarar da ta afkawa kasar.

Daga watan Oktoban bara zuwa yanzu mutane dubu 15 suka harbu da cutar yayinda wasu 32 suka mutu, kuma birnin na Nampula shi ne kan gaba wajen yawan masu fama da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.