Isa ga babban shafi

Wane hali ake ciki a Rwanda shekaru 30 bayan kisan kare dangin 'yan kabilar Tutsi

Al’ummar Rwanda sun wayi garin yau da fara gagarumin bikin tunawa da mutane sama da dubu 800 da suka gamu da ajalin su a sanadin kisan kare dangin da ‘yan kabilar Huti da hadin gwiwar sojojin ketare suka yiwa ‘yan kabilar Tutsi.

Har yanzu babu cikakkiyar kididdigar mutanen da suka mutu a wannan rikici
Har yanzu babu cikakkiyar kididdigar mutanen da suka mutu a wannan rikici © AFP / YASUYOSHI CHIBA
Talla

Yau 7 ga watan Afrilu ne ake cika shekaru 30 cif-cif da faruwar rikicin, da ya zama daya daga cikin tashin hanakali mafi muni da wata kabila ta gani a duniya.

Masana tarihi sun ce har yanzu Rwanda bata gama farfadowa daga bala’in da wannan tashin hankali ya jefa ta ba a shekarar 1994.

Tarihi ya nuna cewa akwai sa hannun ‘yan siyasa da suka kamanta ‘yan kabilar ta Tutsi da kyankyasai don haka basu da wani amfani illa a kashe su, wannan kalma na cikin babban abinda ya janyo rikici.

An dai shafe tsawon mako guda ana bikin tunawa da mamatan, inda aka bude shi ranar 1 ga watan da muke ciki a wata katafariyar makabarta da aka yi ammanar cewa an binne wadanda suka mutu a wannnan rikici sama da dubu 250, inda shugaban kasar Paul Kagame ya kunna kyandira da kuma ajiye furanni don karrama su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.