Isa ga babban shafi

Kasashen duniya sun gaza dakile kisan kiyashin Rwanda - Macron

Shugaba  Emmanuel Macron ya yi amanna cewa, Faransa da aminanta na kasashen yamma da na Afrika na da damar dakatar da kisan kiyashin Rwanda na 1994, amma ba su aikata hakan ba har aka samu asarar rayukan mutane dubu 800 akasarinsu 'yan kabilar Tutsi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AFP - SAMEER AL-DOUMY
Talla

Kalaman na shugaban Faransa na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin cika shekaru 30 cur a ranar Lahadi mai zuwa da kisan kiyashin na Rwanda.

A ranar Lahadin ne za a wallafa wani jawabi na shugaban na Faransa dangane da kisan kiyashin, inda kuma zai jaddada cewa, lallai kasashen duniya na da  hurumin daukar matakin dakile kisan kare dangin, amma suka yi biris kamar dai yadda wani jami'i a fadar Elysee da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana.

Shugaba Macron ya yi amanna cewa, tun ma gabanin aukuwar kisan kare dangin na Rwanda, kasashen duniya na da kwarewa ta tarihi game da yadda suka ga kashe-kashen kare dangi a wasu kasashen kamar wanda aka yi wa Yahudawa a lokacin yakin duniya na biyu da kuma kisan da aka yi wa Armeniyawa a Daular Uthmaniyya da ke Turkiyya a yakin duniya na farko.

Macron ba zai halarci taron tunanawa da kisan kiyashin Rwanda ba

Kodayake bayanai da ke fitowa daga fadar shugaban na Faransa na cewa, Macron din ba zai samu damar halartar taron tunawa da zagayowar wannan rana ba a Lahadi mai zuwa a birnin Kigali, amma Ministan Harkokin Wajen Kasar, Stephane Sejourne zai  wakilce shi.

A wata ziyara da ya kai Rwanda a shekara ta 2021, shugaba Macron ya amince da rawar da kasarsa ta taka wajen kawar da kai a kisan kiyashin, yana mai cewa, wadanda suka tsira da rayukansu ne kawai za su iya yin afuwa.

Shugaban Rwanda Paul Kagame tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Rwanda Paul Kagame tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron AP - Francois Mori

Kodayake Macron bai nemi afuwa kai-tsaye ba, yayin da shugaban Rwanda Paul Kagame ya hakikance wajen neman kwararan bayanai.

 

Rikicin na Rwanda ya faru a zamanin mulkin Francois Mitterrand da ya jagoranci Faransa a wancan lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.