Isa ga babban shafi

Ana bikin cika shekaru 30 da kisan kare dangi a Rwanda

Rwanda na bikin cika shekaru 30 da rikicin da ya hada kisan kare dangi na kabilar Tutsi da aka shafe tsahon kwanaki 100 ana kisan kai baji ba  bani.

Hotunan mutanen da ake nema ruwa a jallo, sakamakon zarginsu da kisan kare dangi a Rwanda.
Hotunan mutanen da ake nema ruwa a jallo, sakamakon zarginsu da kisan kare dangi a Rwanda. © SIMON WOHLFAHRT/AFP
Talla

Kididdiga ta nuna cewa sama da mutane maza, mata da kananan yara dubu 800 ne suka mutu saboda kisan kare dangin da ‘yan kabilar Hutu da tallafin sojojin wasu kasashe musamman na Faransa suka yi musu.

Rikicin na 1994 ya zama guda daga cikin rikice-rikice mafiya muni a tarihi, inda aka ga ma’aurata da aminan juna sun dauki makami akan juna saboda kabilanci.

Har yanzu kasar bata gama farfadowa daga tashin hankalin da ta tsinci kanta a wannan lokaci ba.

A bikin ranar na yau an hango shugaban kasar Paul Kagame ya kunna kyandira tare da ajiye furanni a wata gagarumar makabarta mai cike da tarihi, wadda aka yi ammanar cewa an binne ‘yan kabilar Tustsi sama da dubu 250.

Duk da rikicin ya faru ne ranar 7 ga watan Afrilu, amma kasar na fara gudanar da bukukuwa tun ranar 3 ga wata don karrama wadanda suka rasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.