Isa ga babban shafi

Sudan ta kudu ta bude bincike kan kisan ɗan jarida Allen na RSF

Mahukuntan Sudan ta kudu sun sanar da bude bincike kan musabbabin mutuwar dan jaridar RSF Christopher Allen da ya rasa ransa a shekarar 2017 wanda a baya hukumomin kasar suka ce an kashe shi ne bisa kuskure lokacin da ya ke nadar rahoto kan rikicin kasar.

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu. © Gregorio Borgia / AP
Talla

Sai dai tun a wancan lokaci kungiyoyin ‘yan jarida da ‘yan fafutuka baya ga uwa uba ita kungiyar 'yan jaridun kasa da kasa ta RSF sun yi amannar cewa da nufi ne aka kashe matashin dan jaridar a wancan lokaci.

Allen mai shekaru 26 dan Birtaniya mai shaidar zama a Amurka an harbe shi ne kuma ya mutu nan ta ke lokacin da ya ke nadar rahoto a wata musayar wuta tsakanin Sojojin kasar da ‘yan tawaye a ranar 26 ga watan Agustan 2017.

Tun a wancan lokaci mahukunta basu tsananta wajen ganin an gudanar da bincike ba,  sai bayan da kasashen Birtaniya da Amurka suka matsa lamba wajen ganin lallai an gudanar da binciken don gano musabbabin mutuwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.