Isa ga babban shafi

Adadin wadanda rikici ke shafa a Sudan ta Kudu ya karu da kaso 35 - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da tashin hankali da kuma yaki ke shafa a Sudan ta Kudu ya karu da kaso 35 a watanni uku na karshen bara.

Dimbin jama'a ne ke cikin bukatar agajin gaggawa a Sudan ta Kudu
Dimbin jama'a ne ke cikin bukatar agajin gaggawa a Sudan ta Kudu REUTERS - JOK SOLOMUN
Talla

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ta Kudu ya ce a watanni uku na karshen bara an sami barkewar rikici sau 233 a sassan kasar, wanda kuma ya shafi mutane 862, cikin su 406 sun mutu sai guda 293 da suka jikkata, yayin da aka yi garkuwa da sama da 100.

Wasu karin mutane 63 sun gamu da cin zarafi, lalata ko kuma yi musu fyade.

A rahoton da ofishin ya fitar, ya ce an samu karin mutanen da suke fadawa cikin tashin hankali matuka, idan aka kwatanta da 2022.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da zabe a bana, na farko tun 2018, wanda aka kara tsakanin shugaba Salva Kiir da Riek Machar, abin da ya kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru 5 ana tafkawa, wanda yayi ajalin dubban mutane.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta gudanar da sintirin tabbatar da zaman lafiya a sassan kasar sama da sau dubu 10 ta sama da ta kasa cikin shekarar da ta gabata.

Sudan ta Kudu na cikin kasashen Afrika da ke fama da tsananin zafi, sauyin yanayi, da kuma fari wanda ke sanadiyyar karuwar talauci da tsananin rayuwa ga jama’ar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.