Isa ga babban shafi

Harin masu dauke da makamai ya kashe mutum 15 a Sudan ta Kudu

Harin masu dauke da makamai ya kashe mutum 15, ciki har da mai mukamin kwamishina a yankin Pibor da ke Sudan ta Kudu, abin da ake ganin ya kara dagula rikicin da ke aukuwa a cikin kasar.

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu kenan
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu kenan AFP
Talla

Sudan ta Kudu da ke fama da rikice-rikicen cikin gida, na fama da tashin hankali tun bayan da ta samun ‘yancin kai daga makwabciyarta Sudan.

Rikicin da ya kunno kai tsakanin ‘yan kabilar Dinka da Nuer, tun daga shekarar 2013 zuwa 2018, ya haifar da asarar rayuka da dama.

Rahotanni sun ce harin kwanton baunan ya rutsa da kwamishinan Boma, lokacin da yake kan hanya tare da tawagarsa daga kauyen Nyat.

Ministan yada labaran kasar, Abraham Kelang, ya ce ana zargin maharan sun fito ne daga kabilar Anyuak.

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2018, ana samun rikice-rikice daga kungiyoyin masu dauke da makamai, abin da ya haifar da asarar dimbin rayuka da kuma tilastawa da dama tserewa daga muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.