Isa ga babban shafi

Gwamnatin Sojin Sudan ta yi watsi da tayin tsagaita wuta a yakin da ta ke da RSF

Gwamnatin Sojin Sudan ta yi watsi da kokarin tsagaita wuta a yakin da ta ke da dakarun RSF duk da shiga tsakanin kasashe da kuma tsanantar kiraye-kirayen ganin bangarorin biyu sun ajje makamai musamman a watan da muke ciki na Ramadana, dai dai lokacin da yunwa ke ci gaba da barazana ga miliyoyin fararen hular da yakin kasar ya tagayyara.

Abdel Fattah al-Burhan, jagoran gwamnatin sojin Sudan.
Abdel Fattah al-Burhan, jagoran gwamnatin sojin Sudan. AP - Marwan Ali
Talla

Janar Abdel Fattah al-Burhan wanda zuwa yanzu dakarunsa suka kwace iko da sassa da dama na birnin Oundurman da ke gab da Khartoum fadar gwamnatin kasar ta Sudan, ya ce dakarunsu baza su sarara ba har sai dakarun na RSF sun janye daga ilahirin yankunan fararen hular da suka kame.

Tun gabanin kamawar watan Ramadan ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci bangarorin da ke yakar junan a Sudan su tsagaita wuta a yakin na watanni 11 saboda watan mai alfarma, a bangare guda kungiyar Save the Children ta koka da yadda yara akalla dubu 230 yanzu haka ke cikin matsannaciyar yunwa.

Wasu daga cikin yara 'yan gudun hijira a Omduman na kasar Sudan.
Wasu daga cikin yara 'yan gudun hijira a Omduman na kasar Sudan. REUTERS - EL TAYEB SIDDIG

Zuwa yanzu dai Sojin Sudan na ci gaba da fadada mamayarsu a yankunan da tun da farko dakarun RSF suka kwace iko da su, dalilin da ake ganin shi ya kara kwarin gwiwa ga bangaren al-Burhan wanda a baya da kansa ya bukaci tsagaita wuta.

Har zuwa yanzu dai babu tsokaci daga bangaren jagoran na RSF Muhammad Hamdan Dagalo, wanda tun a baya ya yi ikirarin cewa a shirye ya ke ya mara baya ga don samun fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu tare da kawo karshen zub da jini.

Akalla mutum miliyan 11 suka fada halin yunwa a Sudan sakamakon yakin wanda ya raba miliyoyin iyalai da gidajensu a ciki da wajen kasar, inda Save the Children ke cewa yanzu haka yunwar ka iya kisa ga mutane akalla miliya 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.