Isa ga babban shafi

Jam'iyyar Inkatha ta kaddamar da yakin neman zabenta a yankin Zulu

Jam'iyyar adawa ta Inkatha Freedom a Afrika ta kudu a yau Lahadi ta kaddamar da yakin neman zabenta mai ban mamaki gabanin babban zaben kasar da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu, inda ta tara dimbin magoya bayanta a wani filin wasa da ke Durban, a tsakiyar kasar Zulu, cibiyar zabe.

Wasu daga cikin magoya bayan Jacob Zuma
Wasu daga cikin magoya bayan Jacob Zuma REUTERS - ROGAN WARD
Talla

Wannan dai shi ne karon farko da jam'iyyar mai kishin kasa wacce ta zo ta 4 a zaben da ya gabata a shekarar 2019, ta shiga zaben kasa tun bayan rasuwarsa a watan Satumba yana da shekaru 95 na shugaban kasar da ya kafa ta Mangosuthu Buthulezi.

Ana hasashen jam’iyyar za ta iya fuskantar sabbin kalubale a lardin KwaZulu-Natal, mafi yawan al'umma a kasar, kuma tungar jam'iyyar ANC mai tarihi, a kan karagar mulki ba tare da tsangwama ba tun 1994.

Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma
Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma AFP - EMMANUEL CROSET

Duk da irin wadan kalubale,jam'iyyar adawa ta farko, wato Democratic Alliance (DA), tana samun goyan baya lokuta zuwa lokuta a wannan yanki.

Wani abin mammaki shine kasancewa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma (2009-2018), wanda ya shiga sabuwar jam'iyya, har yanzu yana da tushe mai karfi a wannan yankin da aka haife shi.

Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma
Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma © Kim Ludbrook / AP

Zuma ya kasance a wannan filin wasa na Moses Mabhida da ya samu halartar magoya baya da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.