Isa ga babban shafi

Yan adawar Ghana sun zabi mace a matsayin mataimakiyar John Mahama

John Mahama, dan takarar adawa a zaben shugaban kasar Ghana da za a yi a watan Disamba, ya sanar a yau Alhamis cewa tsohuwar ministar ilimi Jane Opoku-Agyemang zata kasance mataimakiyarsa har idan ya lashe zaben shugabancin kasar ta Ghana.

Wasu daga cikin magoya bayan yan siyasar kasar Ghana
Wasu daga cikin magoya bayan yan siyasar kasar Ghana REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

A kasar ta Ghana wannan dai shi ne karo na biyu da dan takara John Mahama ke zabar Jane Opoku-Agyemang a matsayin mataimakiyarsa a wannan jam’iyya  mai ra'ayin mazan jiya inda mata ba su da wakilci a harkokin siyasa.

"Amincinta, sadaukarwarta da hangen nesanta don samun kyakkyawar Ghana sun sa ta zama 'yar takarar da za ta kasance tare da ni," in ji dan takara John Mahama a cikin wata sanarwa.

Zauren majalisar kasar Ghana
Zauren majalisar kasar Ghana © Misper Apawu / AP

A wannan zabe da zai hada Mahamudu Bawumia, dan takara musulmi na farko a jam'iyyar New Patriotic Party (NPP) da tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama na jam'iyyar adawa ta NDC zai kasance wani lokaci da yan kasar za su neman canza salon shugabanci ko ci gaba da dorewa a kan wannan makama da Nana Akoufo Ado ya shifuda.

Mahamudu Baduwumia, dan takara a jam'iyyar NPP na kasar Ghana
Mahamudu Baduwumia, dan takara a jam'iyyar NPP na kasar Ghana © Luc Gnago / REUTERS

A shekarar 2022, Ghana ta fuskanci matsalar tattalin arziki mafi muni cikin shekaru da dama,kasar ta fuskanci hauhawar farashin kayayyaki sama da kashi 50%, lamarin da ya tilasta wa kasar da ta yi suna a fanin samar da zinari, mai da kuma koko karbar lamuni na dala biliyan 3 daga asusun IMF, tare da aiwatar da wani gyara na basussuka. .

A lokacin zaben 2020, John Mahama ya riga ya zabi Jane Opoku-Agyemang da ta bayyana tare da shi a matsayin shugaban kasar Ghana idan aka samu nasara.

John Dramani Mahama, dan takara a banagaren yan adawa na kasar Ghana
John Dramani Mahama, dan takara a banagaren yan adawa na kasar Ghana AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO

A nata bangaren jam’iyyar NPP ta tsayar da mataimakin shugaban kasa a yanzu kuma tsohon mataimakin daraktan babban bankin kasa, Mahamudu Bawumia a matsayin dan takarar shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.