Isa ga babban shafi

Ghana na zargin 'yan siyasa da sarakuna kan ayyukan masu hakar ma'adanai

Hukumar kula da gandun daji a Ghana ta zargi 'yan siyasa da sarakunan gargajiya da hura wutar yawaitar masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da ake kira da "Galamsey" a dazukan kasar.

Mata da kananan yara dauke da kwanukan kasa a wata tsohuwar mahakar ma'adanai da ke yankin Tarkwa-Nsuaem na kasar Ghana a shekarar 2014.
Mata da kananan yara dauke da kwanukan kasa a wata tsohuwar mahakar ma'adanai da ke yankin Tarkwa-Nsuaem na kasar Ghana a shekarar 2014. Juliane Kippenberg/Human Rights Watch
Talla

Jaridar Daily Graphic da ke kasar ta ruwaito cewa, a halin yanzu aiyyukan masu hakar ma'adanan sun gurbata dazukan kasar, duk da kokarin da hukumar ke yi akan dakile wannan matsalar.

Ma'aikatan gandun dajin kasar sun damu matuka, kan yadda suke sadaukar da rayuwarsu wurin kama irin wadannan masu hakar ma'adanai, amma daga bisani 'yan siyasa da sarakuna su yi amfani da karfinsu wurin kubutar da su ba tare da barin doka ta yi aiki akansu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.