Isa ga babban shafi

Babban Bankin Ghana ya dakatar da lasisin wasu bankunan Najeriya biyu a kasar

Babban Bankin Ghana ya dakatar da lasisin hada-hadar canjin kukaden ketare na wasu bankunan Najeriya biyu da ke kasar, “First Bank da GT Bank” bisa samunsu da laifin saba ka'ida a gudanar da aikinsu.

Hoto don misali
Hoto don misali REUTERS/Jason Lee
Talla

Babban bankin wanda ya sanar da hakan a yau Talata, ya ce dakatarwar da aka yi wa bankunan na tsawon wata daya ne kuma zai fara aiki daga ranar 18 ga wantan Maris da muke ciki.

A cewar jawabin da bankin ya fitar, “ya samu wasu rassan bankunan masu gudanar da hada-hadar canjin kudaden waje da saba ka’idojin bankin yayin gudanar da hadahadarsu” wadanda bawan binciken da bankin zai gudanar za a maida musu da lasisinsu.

Dakatar da bankunan Najeriyar na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwar hada-hadar canjin kudaden waje ke cike da rashin tabbas, yayin da babban bankin kasar ke kokarin samar da daidaito a kasuwar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.