Isa ga babban shafi

Asusun bada lamuni na IMF zai sake lafta wa Ghana bashi

Majalisar gudanarwar asusun bada lamuni na IMF ta sanar da yin wani zama na musamman a juma’a mai zuwa don sahalewa kasar Ghana karin bashin dala miliyan 600 kan dala biliyan 5.4 da kasar ta kasa biya.

Takardun kudaden kasar Ghana na Cedi.
Takardun kudaden kasar Ghana na Cedi. © REUTERS/Francis Kokoroko
Talla

Ghana ta shiga cikin jerin kasashen da bashi ya yiwa katutu kuma suka kasa biya, amma duk da haka tattalin arzikin ta na ciki matsanancin halin da dole sai an bata bashin.

Ko a makon da ya gabata sai da Ghana ta yi wani taron gaggawa da asusun bada lamunin da kuma kasashen China da Faransa wadanda suke binta bashi kan yadda zata sami sassauci ko kuma karin lokacin biyan bashi, kuma a yayin taron ne aka gano ya zama wajibi a karawa kasar bashi don ta farfado.

Kididdiga ta nuna cewa tun shekarar 2022 Ghana ke rayuwa kachokan kan bashin da take karba daga kasashe da hukumomin bada lamuni, dalili kenan da ya sa ta fada cikin jerin kasashen da bashi yayi musu kanta.

Baya ga matsin tattalin arziki, Ghana na fama da tsadar farashin kayan masarufi da rugujewar kudinta wato Cedi a kasuwar chanji, abinda ke kara tunzura yan kasa wajen yiwa gwamnati bore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.