Isa ga babban shafi

Ghana na dakon kashin farko na bashin dala miliyan 600 daga IMF

Ghana na sa ran asusun ba da lamuni na duniya IMF zai amince da bata kason farko na bashin dala miliyan 600 nan da ranar Laraba, kamar yadda karamin ministan kudi Mohammed Amin Adam ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, bayan da kasar ta nemi dala biliyan uku daga IMF domin bunkasa tattalin arzikinta da ya durkushe. 

Ministan tattalin arzikin Ghana Ken Ofori-Atta.
Ministan tattalin arzikin Ghana Ken Ofori-Atta. © Cooper Inveen/Reuters
Talla

Shugabar asusun IMF, Kristalina Georgieva ta ce masu neman lamuni na kasar Ghana, sun ba da cikakkun bayanan da ya kamata ga hukumar gudanarwar IMF, domin duba wa kafin a rattaba hannu kan wannan lamuni. 

Karamin ministan kudin kasar ya ce ana sa ran za a amince da kashi na biyu na dalar Amurka miliyan 600 bayan an yi nasarar yin nazari na farko a shirin, inda za a mika musu sauran wato dala miliyan 360 bayan sake duba shirin bunkasa tattalin arziki da asusun ke yi na shekara-shekara. 

Wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya kan shirin Asusun sun tabbatar da cewa ana sa ran kwamitin zartarwa na masu ba da lamuni zai gana da wakilan Ghana a ranar Laraba. 

Asusun na IMF zai kara habaka asusun Ghana tare da taimaka mata wajen cimma burin samun kudaden ajiyar kasashen waje ta hanyar shigo da kaya nan da shekarar 2026. 

Kamar sauran kasashe masu tasowa da suka hada da Sri Lanka da Zambia, Ghana na fuskantar matsalar bashi bayan da ta riga ta fada matsin tattalin arziki sakamakon annobar COVID-19 da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.