Isa ga babban shafi
Ghana

Asusun IMF ya hana Ghana biyan basukan ketare saboda matsalar tattalin arziki

Ghana ta sanar da dakatar da shirin biyan basukan da kasashen ketare ke bin ta ciki har da na Turai, bayan bukatar da ta mika kan sauya fasalin tsarin biyan bashin lamarin da ke zuwa bayan wata yarjejeniyarta da asusun bada lamuni na Duniya IMF cikin makon jiya.

Shugaban kasar Ghana Nana-Akufo Addo lokacin da ya ke gabatar da sabon tsarin dakatar da biyan basukan da kasashe ke bin kasar.
Shugaban kasar Ghana Nana-Akufo Addo lokacin da ya ke gabatar da sabon tsarin dakatar da biyan basukan da kasashe ke bin kasar. © Mandel Ngan/Reuters
Talla

Bayan doguwar tattaunawar da ta kai ga kulla yarjejeniya tsakanin IMF da Ghana mai fama da mashassharar tattalin arziki, asusun ya gindayawa kasar sharuddan dakatar da biyan basukanta na ketare don samun damar murmurowa daga koma bayan da kasar ke gani ta fannin tattalin arziki.

Wata sanarwa da ma’aikatar kudin Ghana ta fitar ta ruwaito ministar kudin kasar Ken Ofori-Atta na bayyana shirin tsagaita biyan basukan na dan wani lokaci don samun damar farfadowa daga koma bayan tattalin arzikin da kasar ke fama da shi.

Sanarwar ta ce daga jiya litinin Ghana za ta dakatar duk wasu biyan bashi da ta ke kan yi har zuwa lokacin da al’amuran tattalin arziki za su daidaita a kasar.

Yanzu haka dai manyan kungiyoyin kwadagon Ghana sun yi kiran shiga yajin aikin gama gari daga mako mai zuwa domin nuna adawa da shigar da kudaden fanshon ma’aikata a cikin shirin musanya basussukan cikin gida a wani bangare na sharuddan IMF ga kasar.

Kasar Ghana da ke kan gaba wajen samar da koko da gwal, na da dumbin arzikin man fetur da iskar gas, amma hanyar samun kudin shigarta yayi rauni, yayin da ta ke biyan dumbin basuka, matsalolin da aka danganta da annobar korona da kuma yakin Ukraine.

Al'ummar kasar ta Ghana dai na fuskantar tsananin matsin rayuwa da kuma matsanancin koma bayan tattalin arziki bayan da tsadar kayaki ta karu da kashi 50 haka zalika darajar kudin kasar ta karye da kashi 50 baya ga rashin tabbas a farashin man fetur da ke ci gaba da tashi a kowacce rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.