Isa ga babban shafi

'Yan Ghana sun gaji da shugaban kasarsu saboda tsadar rayuwa

Daruruwan 'yan Ghana sun fantsama kan titunan birnin Accra, suna kira ga shugaban kasar, Nana Akufo-Addo da ya yi murabus sakamakon tsadar rayuwa da kuma gazawar gwamnatinsa wajen tunkarar matsalar tattalin ariki.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Ghana
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Ghana REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

A makon da ya gabata ne shugaba Akufo-Addo ya roki 'yan kasar da su amince da shirinsa na karbo bashi daga Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF duk da cewa, wani lokaci a can baya, ya taba yi wa 'yan kasar alkawarin cewa, ba za su ciyo basuka ba.

Yanzu haka dai matsalar tattalin arziki ta shafi kusan kowanne bangare na al'ummar kasar ta Ghana da suka hada da masu hali da talakawa.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka zanta da manema labarai sun ce, babu abin da suke son gani face shugaban kasar da wasu mukarrabansa su yi murabus saboda sun gaji da yadda kasar ke tafiya a cewarsu.

Ghana dai na neman rancen Dala biliyan 3 daga Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF domin shawo kan matsalar hau-hawan farashi da kashi 37  da kuma magance zubewar darajar kudin kasar na Cedi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.