Yunwa ce ke tilasta wa 'yan mata zaman daduro a Ghana
Wani bincike ya nuna cewa, yunwa da talauci na tilasta wa 'yan mata masu kananan shekaru zaman daduro da samarinsu a Ghana, yayin da wasu 'yan matan ake yi musu auren dole saboda gudun cikin-shege.
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:59
Binciken da hukumar GSS ta gudanar ya nuna cewa, akalla 'yan mata dubu 80 ne ke irin wannan zaman na daduro da kuma auren dole a fadin Ghana, kuma shekarunsu bai wuce tsakanin 12 zuwa 17 ba.
Wasu daga cikin iyayen yaran sun ce, gudun kada 'ya'yansu su kawo musu cikin shege gida ne ya sa suke aurar da su da wuri.
Daya daga cikin 'yan matan da muka zanta da su ta ce, lallai talauci ne ya sa take zaman daduro da saurayinta wanda ta ce, yana ba ta abincin safe da rana da dare.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton daga wakilinmu Abdallah Sham'un Bako
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu