Isa ga babban shafi

Tattalin arziki: Ghana ta zaftare albashin shugaban kasa da mukarrabansa

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya sanar da zaftare kasafin kudin kasar da akalla kashi 30 cikin 100 ciki har da rage albashin shugaban kasa da na mataimakinsa da kuma ministoci a kokarin magance matsalar da ta dabaibaye tattalin arzikin kasar.

Shugaba Nana Akufo-Addo.
Shugaba Nana Akufo-Addo. AFP - CRISTINA ALDEHUELA
Talla

Shugaba Nana Akufo-Addo a jawabin da ya gabatar ya ce ko shakka babu kasar ta fada halin matsin tattalin arziki mafi muni wanda ya tilasta dole a dauki matakan gyara don kaucewa sake tsanantar halin da ake ciki.

A cewar shugaba Nana, kasar za ta karfafa samar da kayakin cikin gida tare da rage dogaro da ketare wanda zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin da ke cikin masasshara a yanzu.

Nana Akufo-Addo ya ce baya ga shi kansa da mataimakinsa da kuma ministoci da mataimakansu wadanda zaftare albashin zai shafa za kuma a rage albashin dukkanin masu rike da mukaman siyasa a kowanne mataki.

Shugaban ya ce Ghana bata taba samun kanta a cikin yanayin da tarin shaidanu daga sassa daban-daban suka tattaru tare da hada karfinsu don yunkurin durkusar da kasar ba.

Nana Akufo-Addo ya ce makircin shaidanun zai zamewa kasar alfanu ta yadda za ta samar da damarmakin habaka tattalin arzikinta tare da dawo da kimar kudinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.