Isa ga babban shafi

Kotun Tunisia ta aike da tsohon shugaban kasar gidan yari na shekaru 8

Wata kotu a Tunisia, ta yankewa tsohon shugaban kasar, Moncef Marzouki hukuncin daurin shekaru 8 a gidan yari duk kuwa da cewa baya kasar.

Tsohon shugaban Tunisia Moncef Marzouki kenan.
Tsohon shugaban Tunisia Moncef Marzouki kenan. REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Kotun ta kama Marzouki wanda yanzu haka ya nemi mafaka a Faransa, da laifin cin amanar kasa da yunkurin haddasa tarzoma da tashin hankali ta hanyar kira da ayi juyin mulki a kasar.

Da yake karin haske, mai magana da yawun kotunan kasar Mohammed Zaitouna, ya ce wadannan kadan ne daga cikin laifukan da ake tuhumar tsohon shugaban kasar da aikatawa.

A nasa jawabin, lauyan tsohon shugaban, Samir Ben Amor ya ce wannan hukunci ya nuna irin yadda gwamnatin ke take abokan adawa da kuma cin zarafin su.

Marzouki ya rike jagorancin kasar a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2014, bayan rikicin yankin larabawa da ya tilastawa shugaban kasar Zine El Abidine Ben Ali sauka daga mukamin sa sannan ya bar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.