Isa ga babban shafi

La Francophonie na kokarin warware rikice-ricen kasashen Afirka

Yayin da ake fuskantar kiraye-kirayen a kara kaimi wajen magance rikice-rikicen duniya, shugabannin kasashen duniya masu magana da harshen Faransanci sun gana a Tunisiya ranar Lahadi don tattaunawa kan karuwar rashin zaman lafiya da jin dadin al’ummar nahiyar Afirka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da babar sakatariyar La Francophonie Louise Mushikiwabo da kuma shugaban kasar Tunisiya Kaïs Saied yayin taron kungiyar kasashe masu magana da Faransanci. 19/11/22
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da babar sakatariyar La Francophonie Louise Mushikiwabo da kuma shugaban kasar Tunisiya Kaïs Saied yayin taron kungiyar kasashe masu magana da Faransanci. 19/11/22 AP - Hassene Dridi
Talla

Sai dai an shiga runadani yayin taron da kungiyar La Francophonie ta duniya da aka gudanar a kasar Tunusia, inda da firaministan Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Jean-Michel Sama Lukonde ya ki tsayawa kusa da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame lokacin daukar hoto saboda takun-tsakar kasashen biyu.

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta na zargin Rwanda da goyon bayan 'yan tawayen M23 da suka kwace yankuna da dama a yankinta na gabashin kasar, lamarin da ya raba dubun dubatar mutane da muhallansu a yankin.

Shugabar kungiyar ta IOF mai mambobi 88, Louise Mushikiwabo, ta bayyana cewa "dukkan yankunan da ake fama da rikici abin tada hankali ne, kuma kungiyar a shirye take ta shiga tsakani don sulhunta dukkan bangarori dake adawa da juna.

Rashin karfin fada aji

Ana zargin kungiyar mai kasafin kudinta na shekara-shekara na kasa da Euro miliyan 100, da rashin karfin fada a ji a yankin da aka amfani da harshen faransanci saboda yadda magudin zabe da juyin Mulki dadewa a kan mulki suka mamaye akasarin kasashe mambobinta.

IOF, wanda aka kafa a shekarar 1970, na da nufin haɓaka harshen Faransanci, haɗin gwiwar tattalin arziki da kuma taimakawa wajen sasanta rikice-rikice na duniya.

Shugabannin kasashen Afirka da dama dai sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda kasashen yammacin duniya ke daukar matakin gaggawa kan yakin Ukraine, sabanin rigingimun da ake yi a kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.