Isa ga babban shafi

Annobar Cholera ta kashe mutane fiye da 700 cikin watanni 5 a Zambia

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta Doctors Without Borders ta sanar da mutuwar mutane 700 a sakamakon cutar amai da gudawa daga watan Janairu zuwa yanzu a kasar Zambia.

Har yanzu dai ba'a kai ga shawo kan cutar mai saurin kisa ba
Har yanzu dai ba'a kai ga shawo kan cutar mai saurin kisa ba REUTERS - NAMUKOLO SIYUMBWA
Talla

Kididddiga ta nuna cewa cutar ta kama mutane sama da dubu 20 tun daga lokacin da ta barke a watan Octoban bara.

Bayanai sun ce cutar ta mamaye dukannin yankunan kasar, duk da kokarin da mahukunta suka yi na ganin an dakile ta a manyan biranen Lusaka da Ndola, birane mafiya girma da yawan jama’a a kasar.

Jami’an kiwon lafiya sun ce tuni cutar ta fantsama zuwa kasashen Zimbabwe, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da kuma Malawi.

‘Yan adawa sun zargi gwamnatin Hakainde Hichilema da sakaci wajen shawo kan cutar, dalilin da ya sa ta fantsama a kasar, abinda ya tilasta mayar da manyan guraren taron jama’a da filayen wasanni guraren ajiye marasa lafiya, la’akari da yadda asibitoci suka cika makil.

A watan Janairun da ya gabata, gwamnatin kasar ta fara gangamin rigakafin cutar, wanda aka yi kiyasin yiwa mutane miliyan daya da rabi da ke zaune a gurare masu hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.