Annobar cutar cholera ta kashe mutane 426 a Kamaru
Ma’aikatar lafiyar Kamaru ta tabbatar da yadda annobar cutar Cholera ta kashe mutanen da yawansu ya haura 400 daga lokacin barkewar cutar zuwa yanzu.
Wallafawa ranar:
Bayan karuwar mutanen da cutar ta kashe a makwanni biyu da suka gabata da adadin mutane 26 alkaluman wadanda suka mutu sanadiyyar annobar ta Cholera a sassan kamaru ya karu zuwa mutum 426.
Tun a watan Oktoban shekarar 2021 ne Kamaru ta fara ganin annobar cutar ta Cholera amma kuma a watan Maris din shekarar nan ne cutar ta matukar tsananta inda yanzu haka mutane dubu 1 da 868 ke jinya bayan kamuwa da cutar.
Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa, cutar ta zarta lokacin da bisa al’ada ta kanyi tafiyar hawainiya gabanin yaduwa, Wanda ken una bukatar daukar matakan gaggawa don dakile ci gaba da yaduwarta.
WHO ta ce barkewar cutar a wannan lokacin babban abin fargaba ne, kasancewar ana ci gaba da samun bullarta a kasashen makwabta.
Mahukuntan Lafiyar Kamaru sun ce kashi 79 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar sun samu kulawar lafiya dalilin da ya taimaka wajen dakile yaduwarta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu