Isa ga babban shafi

Tsohon ministan harkokin wajen Burkina Faso ya shaki iskar 'yanci

Tsohon ministan harkokin a Burkina Faso, Ablasse Ouedraogo, ya fito bainar jama’a a wani abu da ke tabbatar da kasancewar sa a raye.

Tsohon ministan harkokin wajen Burkina Faso, Ablasse Ouedraogo kenan.
Tsohon ministan harkokin wajen Burkina Faso, Ablasse Ouedraogo kenan. rfi/Carine Frenk
Talla

 

Tsohon ministan harkokin wajen kasar ya shiga hannun jami’an tsaro ne tun ranar 24 ga watan Disamban 2023, kuma tun lokacin ba’a sake jin duriyar sa ba sai a wannan lokaci.

Jami’an tsaro sun kama shi ne bayan da ya matsa lamba wajen caccakar gwamnatin sojin kasar game da karuwar ayyukan ta’addanci.

A cikin faifan bidiyon dai, an gano cewa tsohon ministan na bakin daga, inda yake yaki da ‘yan ta’adda da nufin tilasta masa bada gudunmowar da yake cewa sojoji basa bayarwa.

Masu sharhi dai na ganin sakin faya-fayan bidiyon ministan wani gargadi ne da gwamnatin sojin ke yiwa masu shirin yi mata katsalandan a aikin ta musamman na tabbatar da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.