Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta ce dakarun Rasha na iya taimaka mata a yaki da 'yan ta'ada

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore ya ce babu sojojin Rasha da ke yaki  da ta’addanci a kasar a halin yanzu, sai dai bai yanke kaunar yin hakan a nan gaba ba. 

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahima Traoré.
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahima Traoré. © Kilaye Bationo / AP
Talla

A makon da ya gabata ne wasu kafafen yada labarai suka ruwaito cewa akwai sojojin Rasha guda 100 da aka shigo da su kasar don yaki da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, lamarin da ya janyo muhawwara. 

 

Traore, wanda ya kwace ragamar mulki a shekarar 2022 ya mayar da hankalinsa ne a kan abin da ya shafi kawar da matsalar tsaro a kasar da ke yankin Sahel.

 

Kuma a ganawar da aka yi da shi a tashar talabijin ta kasar ya ce idan da bukatar shigo da dakarun Rasha don yakar matsalar tsaro a nan gaba, za a yi. 

 

Tarore ya dakarun Rasha da ke kasar su na taimakawa ne da aikin horar da sojojin kasarsa, ba tare da sanya hannu a yakin da suke da ‘yan ta’adda ba.

 

Burkina Faso ta shafe shekaru tana fama da rikicin ta’addanci, sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyar IS, wadanda kuma tuni suka fara  aiki a kasashen Mali da Nijar.

 

Tun da sojoji a karkashin Kyaftin Traore suka karbe mulki  a watan Satumban shekarar 2022, Burkina Faso ta nesanta kanta da tsohuwar uwargijiyarta  Faransa, ta kuma karkata ga Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.