Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta yi watsi da koken ECOWAS kan zargin tabarbarewar tsaro a Kasar

Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta yi watsi da kalaman ECOWAS wanda ke bayyana damuwa kan sake tabarbarewar tsaro a kasar ta yankin Sahel, batun da Ouagadougou ke cewa babu gaskiya a rahotannin baya-bayan nan da ke bayyana tsanantar hare-haren ‘yan ta’adda.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan. © AFP
Talla

Sanarwar da Burkina Faso ta fitar bayan rahotannin da ke bayyana hare-haren ta’addanci kan sojojinta, ta ce abin mamaki ne matuka yadda ECOWAS ta bi sahun wasu kasashe wajen amannar cewa matsalolin tsaro na ta’azzara a kasar.

A cewar gwamnatin Sojin ta Burkina karkashin jagorancin Kyaftin Ibrahim Traore, batu ne da babu ko tantama sojin kasar na samun gagarumar nasara a yakinsu da ‘yan ta’adda ta yadda yanzu haka suka kwato yankuna masu yawa da a baya ke hannun ‘yan ta’addan masu ikirarin jihadi.

Sanarwar da ECOWAS ke fitar kan halin da ake ciki a Burkina Fason na zuwa ne bayan kungiyar tun farko ta shiga sahun masu caccakar kasar ta yammacin Afrika game da muzgunawa kungiyoyin fararen hula baya ga take hakkin fadin albarkacin baki, zarge-zargen da tuni gwamnatin Sojin ta yi watsi da su.

Cikin sanarwar gwamnatin ta bukaci kungiyar wadda tun farko ke samun takun saka da kasar sakamakon juyin mulkin Soji har sau 2 cikin shekara guda, kan ta rika gudanar da binciken kai da kai gabanin kafa hujja da wasu rahotanni wajen sukar kasar.

A cewar gwamnatin Sojin maimakon ci gaba da sukar kasar, lokaci ya yi da ya kamata ECOWAS ta fara jinjinawa namijin kokarin da Sojojin kasar ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.